RAYUWAR KIRISTA
Ku Yi Shiri Yanzu Don Jinyar Gaggawa
Me ya sa yake da muhimmanci mu kasance a shirye? Jinyar gaggawa ta kan zo ba zato ba tsammani. Saboda haka, kafin yanayin gaggawa ya taso, yana da kyau mu kasance a shirye don mu sami kulawar da ta dace idan bukata ta taso. Yin hakan zai nuna mun daraja rai da kuma dokar Jehobah game da jini.—A. M 15:28, 29.
Me za mu iya yi don mu kasance a shirye?
-
Ku yi adduꞌa kuma ku cika Takardar Izinin Kula da Jinya (katin DPA). a Masu shela da suka yi baftisma za su iya samun katin daga wurin bawa mai kula da littattafai da kuma Katin Gabatarwa (ic) don yaransu
-
Mata masu juna biyu su gaya wa dattawan ikilisiyarsu su ba su takardar Information for Expectant Mothers (S-401). Takardar za ta taimaka musu su yanke shawarwari masu kyau game da duk wata matsalar da za ta iya tasowa a lokacin da suke da juna biyu da kuma lokacin haihuwa
-
Idan za a yi muku jinya da ta shafi batun jini ko kuma a kwantar da ku a asibiti, zai dace ku sanar da dattawa da wuri kuma ku gaya wa likitan cewa wani Mashaidi zai zo ya ziyarce ku
Ta yaya dattawa za su taimaka? Za su iya taimaka muku wajen cika katin DPA. Amma, dattawa ba za su yanke muku shawara game da jinya ba ko kuma su cusa muku raꞌayinsu game da shawarar da za ku yanke da kanku ba. (Ro 14:12; Ga 6:5) Idan kun sanar da dattawa cewa za ku yi jinyar da ta shafi batun jini, za su yi magana da Kwamitin Hulɗa da Asibitoci (HLC) nan da nan a madadinku.
Ta yaya HLC za su taimaka? An koyar da ꞌyanꞌuwan da suke hidima a HLC game da yadda za su taimaka wa likitoci da lauyoyi su fahimci raꞌayinmu game da batun jini. Za su iya tattaunawa da likitanku game da yadda zai iya yi muku jinya ba tare da jini ba. Idan da bukata, za su iya taimaka muku ku sami likitan da zai iya muku aiki ba tare da jini ba.
KU KALLI BIDIYON NAN TA YAYA ZA MU YANKE SHAWARWARI GAME DA JINYAR DA TA SHAFI JINI? SAI KU TATTAUNA TAMBAYA TA GABA:
-
Wane darasi ne kuka koya daga bidiyon nan da zai taimaka muku ku kasance a shirye saꞌad da kuke so ku yi jinyar gaggawa da ta shafi batun jini?
a Darasi na 39 na littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! zai taimaka muku ku san shawarar da za ku yanke game da batun da ya shafi jini.