Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ku Yi Amfani da Ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki Ku Taimaka Wa Yaranku

Ku Yi Amfani da Ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki Ku Taimaka Wa Yaranku

Iyaye suna so yaransu su ji daɗi kuma su yi nasara a hidimarsu ga Jehobah. Iyaye za su iya taimaka wa yaransu su yi nasara ta wajen koya musu ƙaꞌidodin Jehobah.​—K. Ma 22:6.

  • Ku sa yaranku su saki jiki da ku kuma su riƙa magana da ku a sake.​—Yak 1:19

  • Ku riƙa yin abubuwa masu kyau don yaranku su koya.​—M.Sh 6:6

  • Ku riƙa yin ibada babu fashi.​—Afi 6:4

KU KALLI BIDIYON NAN KU GINA GIDAN DA ZAI DAWWAMA​—KU KOYA WA YARANKU ‘HANYAR DA ZA SU BI,’ SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Ta yaya iyaye za su nuna sanin ya kamata?

  • Ta yaya iyaye za su bi ƙaꞌidar da ke Yakub 1:19?

  • Me iyaye za su yi idan matsala ta taso?