RAYUWAR KIRISTA
Jehobah Yana Taimaka Mana Saꞌad da Muke Cikin Matsala
A wannan kwanaki na ƙarshe, muna fuskantar matsaloli da yawa. A wasu lokuta, muna iya ganin kamar ba za mu iya jimre matsalolinmu ba. Amma idan muka ci gaba da kusantar Jehobah, zai taimaka mana mu jimre ko da matsalar mai wuya ce sosai. (Ish 43:2, 4) Ta yaya za mu kusaci Jehobah saꞌad da muke cikin matsala?
Adduꞌa. Idan muka gaya wa Jehobah abin da ke damunmu, zai ba mu kwanciyar hankali kuma zai taimaka mana mu jimre.—Fib 4:6, 7; 1Ta 5:17.
Taro. Muna bukatar koyarwar da ke cikin Littafi Mai Tsarki sosai yanzu da kuma yin cuɗanya da ꞌyanꞌuwa a taro. (Ibr 10:24, 25) Idan muka shirya, muka halarci, kuma muka yi kalami a ikilisiya, hakan zai sa mu amfana sosai daga taimakon ruhun Jehobah.—R. Yar 2:29.
Waꞌazi. Zai yi mana sauƙi mu mai da hankali a kan abubuwa masu kyau idan muna iya ƙoƙarinmu mu fita waꞌazi. Hakan zai sa dangantakar mu da Jehobah da kuma ꞌyanꞌuwanmu su yi ƙarfi sosai.—1Ko 3:5-10.
KU KALLI BIDIYON NAN JEHOBAH ZAI KULA DA KAI, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
-
Me ya taimaka wa Malu ta kusaci Jehobah saꞌad da take fama da matsaloli?
-
Ta yaya kalmomin da ke Zabura 34:18 za su taimaka mana saꞌad da muke fuskantar matsaloli kamar yadda ya taimaka wa Malu?
-
Ta yaya labarin Malu ya nuna cewa Jehobah yana ba mu ƙarfin jimre matsaloli?—2Ko 4:7