29 ga Janairu–4 ga Fabrairu
AYUBA 40-42
Waƙa ta 124 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)
1. Darussa da Za Mu Iya Koya Daga Labarin Ayuba
(minti 10)
Ku tuna cewa ba za mu iya sanin yawan abin da Jehobah ya sani ba (Ayu 42:1-3; w10 10/15 3-4 sakin layi na 4-6)
Ku riƙa amincewa da gargaɗi da Jehobah da ƙungiyarsa suke ba mu (Ayu 42:5, 6; w17.06 25 sakin layi na 12)
Jehobah yakan sāka ma waɗanda suka kasance da aminci a gare shi saꞌad da suke cikin matsaloli (Ayu 42:10-12; Yak 5:11; w22.06 25 sakin layi na 17-18)
2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
(minti 10)
-
Ayu 42:7—Game da waye ne abokan Ayuba uku suke magana, kuma ta yaya sanin hakan zai taimaka mana mu jimre idan aka yi mana baꞌa? (it-2-E 808)
-
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?
3. Karatun Littafi Mai Tsarki
(minti 4) Ayu 42:1-17 (th darasi na 11)
4. Fara Magana da Mutane
(minti 3) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Mutumin ba Kirista ba ne. (lmd darasi na 5 batu na 3)
5. Almarjirtarwa
6. Jawabi
(minti 4) lmd ƙarin bayani na 1 batu na 2—Jigo: Ba Za a Taɓa Hallaka Duniyar Nan Ba. (th darasi na 13)
Waƙa ta 108
7. Ku Taimaka wa Mutane Su San Cewa Jehobah Yana Ƙaunar Su
(minti 15) Tattaunawa.
Muna farin ciki cewa muna bauta wa Allah wanda yake ƙaunar mutane. (1Yo 4:8, 16) Yadda Jehobah yake ƙaunarmu ne yake sa mu so zama abokansa kuma hakan na sa mu ƙarfafa dangantakarmu da shi. Da yake mu bayin Jehobah ne, yana ƙaunar dukanmu.
Ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu, mu yi koyi da Jehobah kuma mu riƙa ƙaunar mambobin iyalinmu da ꞌyanꞌuwa da kuma sauran mutane. (Ayu 6:14; 1Yo 4:11) Ta wurin ƙaunar mutane, muna taimaka musu su san Jehobah kuma su ƙulla dangantaka da shi. Amma idan mun ƙi mu ƙaunaci mutane, zai yi musu wuya su gaskata cewa Jehobah yana ƙaunarsu.
Ku kalli BIDIYON An Nuna Mana Ƙauna Ta Gaskiya a Ƙungiyar Jehobah. Sai ka tambayi masu sauraro:
Mene ne kuka koya daga labarin Lei Lei da Mimi da ya nuna muhimmanci nuna ƙauna?
Mene ne za mu iya yi don mu taimaka wa ꞌyanꞌuwanmu su san cewa Jehobah yana ƙaunarsu?
-
Ku riƙa ganinsu a matsayin bayin Jehobah masu tamani.—Za 100:3
-
Ku riƙa yi musu magana a hanyar da za ta ƙarfafa su.—Afi 4:29
-
Ku yi ƙoƙari ku fahimci yadda suke ji.—Mt 7:11, 12