Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

10-16 ga Fabrairu

ZABURA 147-150

10-16 ga Fabrairu

Waƙa ta 12 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

1. Muna da Dalilai da Yawa na Yabon Jehobah

(minti 10)

Yana kula da kowannenmu (Za 147:​3, 4; w17.07 18 sakin layi na 5-6)

Ya san yadda muke ji kuma yana amfani da ikonsa don ya taimaka mana (Za 147:5; w17.07 18 sakin layi na 7)

Ya ba mu gatan zama mutanensa (Za 147:​19, 20; w17.07 21 sakin layi na 18)


KA TAMBAYI KANKA, ‘Wane abu ne kuma yake sa na yabi Jehobah?’

2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah

(minti 10)

  • Za 148:​1, 10—Me muka koya game da Jehobah daga yadda “tsuntsaye masu fikafikai” suke kaura? (w23.03 17 sakin layi na 6)

  • A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?

3. Karatun Littafi Mai Tsarki

(minti 4) Za 148:1–149:9 (th darasi na 11)

KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO

4. Fara Magana da Mutane

(minti 3) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Mutumin ya gaya maka cewa yana da ciwo mai tsanani. (lmd darasi na 2 batu na 5)

5. Fara Magana da Mutane

(minti 4) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka nemi damar gaya wa mutumin wani abu da ka koya a taronmu na kwana-kwanan nan. (lmd darasi na 4 batu na 3)

6. Jawabi

(minti 5) w19.03 10 sakin layi na 7-11—Jigo: Ku Saurari Yesu —Ku Yi Waꞌazi. Ka duba hoto. (th darasi na 14)

RAYUWAR KIRISTA

Waƙa ta 159

7. Rahoton Hidima na Shekara-Shekara

(minti 15) Tattaunawa.

Bayan ka karanta wasiƙar da aka aiko daga ofishinmu game da rahoton hidima na shekara-shekara, ka gaya wa masu sauraro su ambata wasu fannoni masu kyau da ke Rahoton Hidima na Shekara-shekara na Shaidun Jehobah na 2024. Ka gana da wasu masu shela da ka zaɓa da suke da labarai masu kyau game da wa’azi da suka yi a shekarar hidima da ta shige.

8. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya

Kammalawa (minti 3) | Waƙa ta 37 da Adduꞌa