Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

20-26 ga Janairu

ZABURA 138-139

20-26 ga Janairu

Waƙa ta 93 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

1. Kada Ka Bar Tsoro Ya Hana Ka Yin Kalami A Taro

(minti 10)

Muna so mu yabi Jehobah da dukan zuciyarmu (Za 138:1)

Idan kana jin tsoron yin kalami a taro, ka roƙi Jehobah ya taimaka maka (Za 138:3)

Jin tsoron yin kalami ba laifi ba ne (Za 138:6; w19.01 10 sakin layi na 10)

SHAWARA: Yin gajeren kalami zai taimaka maka ka rage jin tsoro.—w23.04 21 sakin layi na 7.

2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah

(minti 10)

  • Za 139:​21, 22—Shin ana bukatar Kiristoci su gafarta wa kowa da kowa ne? (it-1-E 862 sakin layi na 4)

  • A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?

3. Karatun Littafi Mai Tsarki

(minti 4) Za 139:​1-18 (th darasi na 2)

KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO

4. Fara Magana da Mutane

(minti 3) WAꞌAZI A INDA JAMAꞌA SUKE. (lmd darasi na 2 batu na 3)

5. Almajirtarwa

(minti 4) WAꞌAZI A INDA JAMAꞌA SUKE. Ka nuna yadda muke gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki. (lmd darasi na 10 batu na 3)

6. Jawabi

(minti 5) ijwyp talifi na 105—Jigo: Me Zan Yi Don In Rage Jin Kunya? (th darasi na 16)

RAYUWAR KIRISTA

Waƙa ta 59

7. Za ka Iya Jin Daɗin Hidimarka ko da Kana Jin Kunya

(minti 15) Tattaunawa.

Shin kai mai jin kunya ne? Ka fi so ka yi shiru a cikin jamaꞌa? Shin gabanka na faɗiwa saꞌad da kake so ka yi magana da mutane? A wasu lokuta, kunya za ta iya hana mu yin abubuwan da muke so mu yi. Amma mutane da yawa da suka yi fama da kunya a dā sun iya shawo kan matsalar, kuma suka ji daɗin hidimarsu. Me za mu koya daga misalinsu?

Ku kalli BIDIYON Na Yi Iya Ƙoƙarina Duk da Kunyar da Nake Ji. Sai ka tambayi masu sauraro:

  • Ta yaya ꞌYarꞌuwa Lee ta amfana don ta bi shawarar kakarta cewa ta “bauta wa Jehobah dukan rayuwarta”?

Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa mutane kamar su Musa da Irmiya da kuma Timoti sun yi fama da kunya. (Fit 3:11; 4:10; Irm 1:​6-8; 1Ti 4:12) Duk da haka, sun yi abubuwa da yawa a hidimarsu domin Jehobah ya taimaka musu. (Fit 4:12; Irm 20:11; 2Ti 1:​6-8)

Karanta Ishaya 43:​1, 2. Sai ka tambayi masu sauraro:

  • Wane alkawari ne Jehobah ya yi wa masu bauta masa?

Ta yaya Jehobah zai taimaka ma waɗanda suke jin kunya su yi nasara a hidimarsu?

Ku kalli BIDIYON Baftisma: Yadda Yin Baftisma Zai Ƙara Sa Ku Farin Ciki—Takaitawa. Sai ka tambayi masu sauraro:

  • Ta yaya ꞌYarꞌuwa Jackson ta ga yadda Jehobah ya taimaka mata a waꞌazi?

  • Ta yaya waꞌazi zai taimaka wa mutum mai jin kunya?

8. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya

Kammalawa (minti 3) | Waƙa ta 151 da Adduꞌa