RAYUWAR KIRISTA
“Kada Ku Damu”
Jehobah ya taimaka wa talakawa a Isra’ila ta dā. A waɗanne hanyoyi ne yake taimaka wa bayinsa talakawa a yau?
-
Ya koya musu su kasance da ra’ayin da ya dace game da kuɗi.—Lu 12:15; 1Ti 6:6-8
-
Ya taimaka musu su san cewa suna da mutunci.—Ayu 34:19
-
Ya koya musu su yi aiki tuƙuru kuma su guji halayen banza.—K. Ma 14:23; 20:1; 2Ko 7:1
-
Ya sa su kasance cikin ƙungiyarsa da ’yan’uwa suke ƙaunar juna.—Yoh 13:35; 1Yo 3:17, 18
-
Ya sa su kasance da bege.—Za 9:18; Ish 65:21-23
Ko da muna cikin yanayi mai wuya, bai kamata mu riƙa yawan damuwa ba. (Ish 30:15) Jehobah zai biya bukatunmu muddin mun sa al’amuran Mulki farko a rayuwarmu.—Mt 6:31-33.
KU KALLI BIDIYON NAN KU NUNA ƘAUNAR DA BA TA ƘAREWA KO DA . . . KUNA FAMA DA TALAUCI—KWANGO, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
-
Ta yaya ’yan’uwan da suke zama kusa da wuraren da ake taron yanki suka kula da ’yan’uwan da suka halarci taron daga wasu wurare?
-
Mene ne bidiyon nan ya koya mana game da yadda Jehobah yake kula da talakawa?
-
Ta yaya za mu iya yin koyi da Jehobah ko da mu talakawa ne ko masu arziki?