KA YI WA’AZI DA KWAZO | YADDA ZA KA DAƊA JIN DAƊIN WA’AZI
Ka Ratsa Zukatan Mutane
Ya kamata mu yi biyayya ga Jehobah da dukan zuciyarmu. (K. Ma 3:1) Saboda haka, sa’ad da muke koyarwa, wajibi ne mu yi ƙoƙarin ratsa zukatan masu sauraronmu. Ta yaya za mu yi hakan?
Sa’ad da kake nazari da ɗalibinka, ka taimaka masa ya ga yadda batun ya shafe shi da kuma dangantakarsa da Jehobah. Ka taimaka masa ya fahimci yadda ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki suka nuna cewa Allah mai ƙauna ne, mai alheri da kuma adalci. Ka yi amfani da tambayoyin da suka dace don ka san yadda yake ji game da abubuwan da yake koya. Ka taimaka masa ya yi tunani yadda rayuwarsa za ta gyaru idan ya canja hali ko ra’ayin da bai dace ba. Idan ka ga yadda ɗalibinka yake ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarsa, hakan zai sa ka farin ciki sosai.
KU KALLI BIDIYON NAN ZA KU JI DAƊIN ALMAJIRTARWA IDAN KUN INGANTA YADDA KUKE WA’AZI—KU RATSA ZUKATAN MUTANE, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
-
Me ya sa Anita ta tambayi Rose cewa: “Kin yi tunani a kan abin da muka tattauna ran Litinin?”
-
Ta yaya Anita ta taimaka wa Rose ta fahimci yadda ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki suka nuna cewa Jehobah yana ƙaunar ta?
-
Ta yaya Anita ta taimaka wa Rose ta san yadda za ta nuna cewa tana ƙaunar Allah?