Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

KA YI WA’AZI DA KWAZO | YADDA ZA KA DAƊA JIN DAƊIN WA’AZI

Kauna da Tausayi

Kauna da Tausayi

Furucin nan ƙauna da tausayi yana nufin fahimtar ra’ayin mutane da yadda suke ji da daraja su da kuma sanin bukatunsu. Mutane sukan san lokacin da muke jin tausayinsu. Idan muna da ra’ayin taimaka wa mutane, za mu tausaya musu. Nuna ƙauna da jin tausayin mutane sa’ad da muke wa’azi ya dace. Domin hakan yana nuna cewa muna yin koyi da halin Jehobah na ƙaunar mutane da kula da su. Kuma zai sa mutane su kusace shi.​—Fib 2:4.

Ba a lokacin da muke koyarwa kawai muke nuna ƙauna da tausayi ba. Amma za mu nuna hakan ta saurarar mutane da kyau, ta furucinmu da halinmu da yadda muke motsa hannayenmu da kuma nuna fara’a. Muna nuna halin nan kuma ta wajen kula da mutane, da yin la’akari da abubuwan da suke so, da abin da suka yi imani da shi, da kuma yanayinsu. Ko da yake muna gaya musu abin da zai taimaka musu, ba za mu tilasta musu su canja ra’ayinsu ba. Za mu yi farin ciki sosai idan mutanen suka soma bauta wa Jehobah.

KU KALLI BIDIYON NAN ZA KU JI DAƊIN ALMAJIRTARWA IDAN KUN INGANTA YADDA KUKE WA’AZI​—KU NUNA ƘAUNA DA TAUSAYI, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Ta yaya Anita ta nuna ƙauna da tausayi a lokacin da Rose ta makara zuwa wurin da suka shirya yin nazari?

  • Ta yaya Anita ta nuna ƙauna da tausayi sa’ad da Rose ta ce ta gāji?

  • Mutane za su so su koya game da Jehobah sa’ad da muka nuna musu ƙauna da tausayi

    Ta yaya Anita ta nuna ƙauna da tausayi sa’ad da Rose ta ce ita ba mai shirya kayayyaki ba ce?