RAYUWAR KIRISTA
Ku Bi da Tsofaffin Mata Kamar Mama, ’Yan Mata Kuma Kamar ’Yan’uwa
Littafi Mai Tsarki ya umurce Kiristoci su bi da tsofaffi kamar mama da baba kuma su bi da waɗanda ba tsofaffi ba kamar ’yan’uwa. (Karanta 1 Timoti 5:1, 2.) Ya kamata ’yan’uwa maza musamman su riƙa daraja mata.
Bai kamata wani ɗan’uwa ya yi wani abu da zai hana wata ’yar’uwa sake jiki sa’ad da take tare da shi ba. (Ayu 31:1) Bai dace ɗan’uwan da ba shi da aure ya sa ’yar’uwar da ba ta da aure ta riƙa ganin kamar yana son ta, amma ba ya son ta da aure.
Ya kamata dattawa su yi la’akari da ’yan’uwa mata da suka nemi ƙarin bayani a kan wani batu, ko kuma suka faɗi wani abu da zai dace su ɗau mataki. Zai dace dattawa su kula da ’yan’uwa mata musamman waɗanda ba su da mijin da zai kāre su.—Ru 2:8, 9.
KU KALLI BIDIYON NAN KU RIƘA NUNA ƘAUNAR DA BA TA ƘAREWA GA ’YAN’UWANMU MASU BI—GWAMRAYE DA MARAYU, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
-
Ta yaya ’yan’uwa a ikilisiya suka nuna wa ’Yar’uwa Myint ƙauna ta musamman?
-
Ta yaya ƙaunar da ’yan’uwan suka nuna ta sa mutanen ƙauyen suka ɗaukaka sunan Jehobah?
-
Ta yaya ƙaunar da ’yan’uwa suka nuna ta shafi yaran ’Yar’uwa Myint?
A waɗanne hanyoyi ne za ka nuna cewa kana daraja ’yan’uwa mata da suke ikilisiyarku?