Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

KA YI WA’AZI DA ƘWAZO

Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Ka Rubuta Taka Gabatarwa

Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Ka Rubuta Taka Gabatarwa

MUHIMMANCINSA: Ko da yake gabatarwar da ake sakawa a wannan littafin taro suna da kyau sosai, amma bai kamata ka haddace su ba. Zai dace ka yi amfani da naka kalmomin. Za ka iya yin amfani da wata gabatarwa ko kuma ka gabatar da wani talifi idan kana gani zai fi amfanar mutane a yankinku. Saboda haka, bayan ka karance mujallar da gabatarwar kuma ka kalli bidiyon gabatarwar, za ka iya yin amfani da shawarar da ke gaba don rubuta taka gabatarwa.

YADDA ZA MU CIM MA HAKAN:

Ka tambayi kanka, ‘Shin ina so in yi amfani da gabatarwar da aka bayar?’

E

  • Ka shirya yadda za ka soma tattaunawar. Bayan ka gai da maigidan, ka ambata dalilin da ya sa ka kawo masa ziyara. (Alal misali: “Na zo don . . . ”)

  • Ka yi la’akari da abin da za ka ce bayan ka yi tambayar, ka karanta nassin kuma ka ba da mujallar. (Alal misali: Sa’ad da kake gabatar da nassin, kana iya cewa: “Za ka iya samun amsa mai gamsarwa a wurin nan.”)

A’A

  • Ka zaɓi talifin da ke cikin mujallar da kake so kuma mutane a yankinku za su so

  • Ka yi tunani a kan tambayar da za ka yi da ba zai kunyatar da maigidan ba, amma zai sa shi tunani kuma ya furta ra’ayinsa. (Alal misali: Tambayoyin da ke shafi na 2 na mujallunmu.)

  • Ka zaɓi nassin da za ka karanta. (Idan mujallar Awake! ce za ka bayar, to, ba lallai sai ka karanta nassi ba domin an shirya shi ne don mutanen da ba su san Littafi Mai Tsarki sosai ba ko kuma ba sa son addini.)

  • Ka faɗi wasu kalmomin da za su taimaka wa maigidan ya ga yadda zai amfana daga mujallar

A DUK YANAYI

  • Ka shirya tambayar da za ka yi sa’ad da ka koma ziyara

  • Ka rubuta bayanan da za su taimaka maka ka tuna da abin da kake son ka faɗa in ka sake dawowa