Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LIVING AS CHRISTIANS

Yadda Za a Yi Amfani da Ka Saurari Allah

Yadda Za a Yi Amfani da Ka Saurari Allah

An shirya ƙasidar nan Ka Saurari Allah don a yi amfani da hotuna wajen koya wa mutanen da ba su iya karatu ba muhimman gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki. Kowane darasi yana ɗauke da shafuffuka biyu da ke da hotuna da kuma alama da za ta nuna yadda za a yi amfani da hotunan ɗaya bayan ɗaya.

Ƙasidun nan Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada da Ka Saurari Allah suna da hotuna iri ɗaya. Amma rubutun da ke Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada ya fi yawa kuma ɗalibi da ya iya karatu zai iya amfani da ita. Masu shela suna yawan amfani da ita sa’ad da suke nazari idan ɗalibin yana amfani da Ka Saurari Allah. Yawancin shafuffukan suna da akwati da ke ɗauke da ƙarin bayani da za a iya tattauna bisa ga fahimtar ɗalibin.

Za ka iya ba da ƙasidar a kowane lokaci, ko idan ba ita ce littafin da ake rarraba a watan ba. Ka yi amfani da hotunan don bayyana labarin da ke Littafi Mai Tsarki. Ka yi amfani da tambayoyi don ka san abin da ke zuciyar ɗalibin kuma ka tabbata cewa ya fahimta sosai. Ku karanta da kuma tattauna nassosin da ke ƙarƙashin kowane shafi. Bayan kun kammala ƙasidar, ku yi nazarin littafin nan Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki? don ɗalibin ya cancanci yin baftisma.