Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 20-21

“Duk Wanda Yake So Ya Zama Babba A Cikinku, Dole Ne Ya Zama Mai Yi Wa Sauran Hidima”

“Duk Wanda Yake So Ya Zama Babba A Cikinku, Dole Ne Ya Zama Mai Yi Wa Sauran Hidima”

20:28

Malamai da Farisawa masu fahariya suna son mutane su riƙa daraja da kuma gaishe su a cikin kasuwa

Malamai da Farisawa masu fahariya sun so mutane su ga kwarjininsa kuma su riƙa daraja su. (Mt 23:​5-7) Amma Yesu ba haka yake ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ɗan mutum ya zo ba domin a yi masa bauta ba, amma domin shi bauta wa waɗansu.” (Mt 20:28) Shin muna mai da hankali ne musamman ga hidimar da za ta sa mu yi suna kuma a riƙa yaba mana? Idan muna son Jehobah ya amince da mu, wajibi ne mu bi misalin Yesu kuma mu riƙa taimaka wa mutane. Kuma Jehobah ne kaɗai yake sanin irin wannan taimakon da muke yi wa mutane. (Mt 6:​1-4) Wanda yake da sauƙin kai yana . . .

  • taimakawa a yin shara da kuma tsabtace Majami’ar Mulki

  • taimaka wa tsofaffi da kuma mutane da yardan rai

  • ba da gudummawa don a samu ci gaba a wa’azi