12-18 ga Maris
MATTA 22-23
Waƙa ta 30 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Ku Riƙa Bin Umurnin Dokoki Biyu Mafi Girma”: (minti 10)
Mt 22:36-38—Ta yaya wannan ayar ta bayyana abin da doka ta farko mafi girma ta ƙunsa? (nwtsty na nazarin Mt 22:37)
Mt 22:39—Mece ce doka ta biyu mafi girma? (nwtsty na nazari)
Mt 22:40—Abubuwan da aka rubuta a duka littattafan Ibrananci game da ƙauna ne (nwtsty na nazari)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Mt 22:21—Mene ne “abin da ke na Kaisar,” da kuma “abin da ke na Allah”? (nwtsty na nazari)
Mt 23:24—Mene ne Yesu yake nufi a ayar nan? (nwtsty na nazari)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Mt 22:1-22
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 2 ko ƙasa da hakan) Ka bi bayanin da ke yadda za mu yi wa’azi.
Bidiyon Komawa Ziyara ta Farko: (minti 5) Ka nuna bidiyon kuma ku tattauna shi.
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 6 ko ƙasa da hakan) bhs 199 sakin layi na 8-9—Mai shelar ya ƙarfafa ɗalibin ya gayyaci mutanen da ya sani zuwa taron Tunawa da Mutuwar Yesu.
RAYUWAR KIRISTA
Waƙa ta 96
“Ta Yaya Za Ka Ƙaunaci Allah da Kuma Maƙwabtanka?”: (minti 15) Tattaunawa. Don ka nuna muhimmancin yin tunani a kan labaran Littafi Mai Tsarki, ka saka bidiyon nan Jehobah Ne Kaɗai Allah Na Gaskiya—Taƙaitawa. Ka gaya wa ’yan’uwa su bi karatun a littafin 1 Sarakuna 18:17-46.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lv babi na 5 sakin layi na 1-6 da akwatin da ke shafi na 52 da 55
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 52 da Addu’a