MATTA 25
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH |“Ku Yi Tsaro”
25:1-12
Ko da yake kwatancin da Yesu ya yi na budurwai goma musamman ga shafaffun Kiristoci ne, amma dukan Kiristoci za su iya koyan darussa daga kwatancin. (w15 3/15 12-16) “Ku yi tsaro fa, gama ba ku san rana ko sa’a ba.” (Mt 25:13) Shin za ka iya bayyana ma’anar kwatancin nan da Yesu ya yi?
-
Angon (aya ta 1)—Yesu
-
Masu hikima, budurwai da suka yi shiri (aya ta 2)—Shafaffun Kiristoci da suka yi shiri don su yi aikinsu da aminci kuma suka ci gaba da haskakawa har zuwa ƙarshe (Fib 2:15)
-
Ji murya: “Ga ango!” (aya ta 6)—Alamar bayyanuwar Kristi
-
Budurwai marasa-azanci (aya ta 8)—Shafaffun Kiristoci da suka fita don su marabci Angon amma ba su ci gaba da yin tsaro da kuma kasancewa da aminci ba
-
Budurwai masu hikiman sun ƙi su ba da mān su (aya ta 9)—Bayan da aka hatimce su a ƙarshe, babu wani lokaci da ya rage don a taimaka wa shafaffun da suka daina kasancewa da aminci
-
“Ango ya zo” (aya ta 10)—Yesu ya zo ya yi shari’a a ƙarshen ƙunci mai girma
-
Da budurwai masu hikima suka shiga wurin biki tare da angon, sai aka rufe kofar (aya ta 10)—Yesu ya tattara shafaffunsa zuwa sama, amma shafaffu marasa aminci sun rasa gādonsu na zuwa sama