Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Yadda Za Mu Yi Wa’azi

Yadda Za Mu Yi Wa’azi

●○○ HAƊUWA TA FARI

Rarraba Takardar Gayyata na Taron Tunawa da Mutuwar Yesu (3-31 ga Maris): Muna gayyatar ka zuwa wani taro na musamman. Ga naka takardar gayyatar. Miliyoyin mutane a duniya za su taru a ranar 31 ga Maris don su Tuna da Mutuwar Yesu. An rubuta lokaci da kuma wurin da za a yi taron a wannan yankin a cikin takardar. Muna kuma gayyatar ka zo ka saurari wani jawabi mai jigo “Shin, Waye ne Yesu Kristi?” Za a ba da jawabin kafin makon da za a yi taron tunawa da mutuwar Yesu.

Tambayar da Za Ka Yi Idan Mutumin Ya So Wa’azin: Me ya sa Yesu ya mutu?

○●○ KOMAWA ZIYARA TA FARKO

Tambaya: Me ya sa Yesu ya mutu?

Nassi: Mt 20:28

Tambaya don Ziyara ta Gaba: Wane abu ne fansa ta cim ma?

○○● KOMAWA ZIYARA TA BIYU

Tambaya: Wane abu ne fansa ta cim ma?

Nassi: Ro 6:23

Tambaya don Ziyara ta Gaba: Ta yaya za mu nuna godiya don fansar?