18-24 ga Maris
1 KORINTIYAWA 1-3
Waƙa ta 127 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Kana Barin Ruhun Allah Ya Yi Maka Ja-goranci Kuwa?”: (minti 10)
[Ka nuna bidiyon Gabatarwar Littafin 1 Korintiyawa.]
1Ko 2:14—Mene ne ake nufi da “mutumin da ba ruhu ne yake bi da shi ba”? (mwbr19.03-HA an ɗauko daga w18.02 19 sakin layi na 4-5)
1Ko 2:15, 16—Mene ne ake nufi da “mutumin da ruhu yake bi da shi”? (mwbr19.03-HA an ɗauko daga w18.02 19 sakin layi na 6; 22 sakin layi na 15)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
1Ko 1:20—Ta yaya Allah ya mai da “hikima ta wannan duniya wawanci”? (mwbr19.03-HA an ɗauko daga it-2 1193 sakin layi na 1)
1Ko 2:3-5—Ta yaya misalin Bulus zai taimaka mana? (w08 7/15 27 sakin layi na 6)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) 1Ko 1:1-17 (th darasi na 10)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Bidiyon Komawa Ziyara ta Farko: (minti 5) Ku kalli bidiyon kuma ku tattauna shi.
Komawa Ziyara ta Farko: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka bi bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. (th darasi na 3)
Komawa Ziyara ta Farko: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Ka bi bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi, kuma ka gabatar da littafin nan Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki? (th darasi na 11)
RAYUWAR KIRISTA
“Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Yadda Za Mu Rubuta Wasiƙu da Kyau”: (minti 8) Tattaunawa.
Za a Soma Rarraba Takardar Gayyata na Taron Tuna da Mutuwar Yesu a Ranar Asabar, 23 ga Maris: (minti 7) Tattaunawar da mai kula da hidima zai yi. A ba kowa kofi guda na takardar gayyatar kuma ku tattauna abin da ke ciki. Ku kalli bidiyon yadda za a yi gayyatar kuma ku tattauna shi. Ka bayyana yadda ikilisiyarku za ta rarraba takardar a yankin gabaki ɗaya.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) bhs babi na 5 sakin layi na 1-8 da ƙarin bayani na 9
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 51 da Addu’a