Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ka Yi Amfani da Bidiyoyi don Ka Koyar da Dalibanka

Ka Yi Amfani da Bidiyoyi don Ka Koyar da Dalibanka

Abubuwan da mutum ya gani suna jawo hankalinsa kuma suna taimaka masa ya tuna abubuwan da ya koya. Jehobah wanda shi ne Malami Mafi Girma ma ya yi amfani da abin da ake gani don ya koyar da darussa masu muhimmanci. (Fa 15:5; Irm 18:​1-6) Yesu, Babban Malami, ma ya yi hakan. (Mt 18:​2-6; 22:​19-21) A ’yan shekarun nan, ɗaya daga cikin abubuwan da ke jan hankalin mutane sa’ad da muke wa’azi shi ne bidiyonmu. Kana yin amfani da bidiyo sosai sa’ad da kake koyar da ɗalibanka?

An shirya bidiyoyi guda goma da za su taimaka mana mu koyar da darussan da ke ƙasidar nan Albishiri Daga Allah! Kowanne bidiyon ya amsa ɗaya daga cikin tambayoyin da ke ƙasidar. A ƙasidar da ke dandalinmu na jw.org/ha, an saka bidiyoyin don ka san lokacin da ya kamata ka nuna kowannensu. Ƙari ga haka, akwai wasu bidiyoyi kuma da suke yin ƙarin haske a kan wasu littattafan da muke wa’azi da su.

Shin kuna tattauna wani batu da zai yi ma ɗalibinka wuyar fahimta? Ko kuma ɗalibinka yana fama da wata matsala? Ka bincika bidiyoyin da ke jw.org® da JW Broadcasting® na Hausa a jw.org/ha da Tashar JW don ka ga wanda zai taimaka masa. Za ku iya kalli ɗaya daga cikinsu tare kuma ku tattauna shi.

A kowane wata, mukan fitar da sabbin bidiyoyi. Yayin da kake kallon su, ka yi tunani a kan yadda za ka yi amfani da su sa’ad da kake koyar da ɗalibinka.