Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARUSSA DAGA LITTAFI MAI TSARKI | ROMAWA 12-14

Yadda Za Mu Nuna Kauna ga ’Yan’uwa

Yadda Za Mu Nuna Kauna ga ’Yan’uwa

12:10, 17-21

Idan muna ƙaunar ’yan’uwanmu, ba za mu rama laifin da suka yi mana ba, sai dai mu sāka musu da alheri. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idan abokin gābanka yana jin yunwa, sai ka ba shi abinci. Idan yana jin ƙishin ruwa, sai ka ba shi ruwan sha. Ta yin haka kana tara garwashin wuta a kansa ne.” (Ro 12:20) Alherin da muka nuna wa mutumin da ya yi mana laifi zai iya sa ya yi da-na-sani.

Yaya ka ji sa’ad da ka yi ma wani laifi cikin rashin sani amma bai rama ba kuma ya yi maka alheri?