9-15 ga Maris
FARAWA 24
Waƙa ta 132 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 1)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“An Samo wa Ishaku Mata”: (minti 10)
Fa 24:2-4—Ibrahim ya aiki bawansa ya nemo wa Ishaku mata da take bauta wa Jehobah (wp16.3 14 sakin layi na 3)
Fa 24:11-15—Bawan Ibrahim ya haɗu da Rebeka a bakin rijiya (wp16.3 14 sakin layi na 4)
Fa 24:58, 67—Rebeka ta yarda ta auri Ishaku (wp16.3 14 sakin layi na 6-7)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 10)
Fa 24:19, 20—Me za mu iya koya daga abin da Rebeka ta yi a waɗannan ayoyin? (wp16.3 12-13)
Fa 24:65—Me ya sa Rebeka ta rufe kanta, kuma wane darasi ne muka koya? (wp16.3 15 sakin layi na 3)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu game da Jehobah Allah da wa’azi da dai sauransu?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Fa 24:1-21 (th darasi na 2)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 4) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon, sai ka yi tambayoyin nan: Ta yaya mai shelan ya yi tambayoyin da suka dace? Mene ne ya yi sa’ad da maigidan ya amsa tambayarsa game da Yesu?
Haɗuwa ta Fari: (minti 2 ko ƙasa da hakan) Ka bi abin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. (th darasi na 1)
Haɗuwa ta Fari: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka soma da bin abin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Mutumin ya ba da wata hujja da mutane suka saba bayarwa. (th darasi na 12)
Gayyata Zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka soma da bin abin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Mai gidan ya so wa’azin. Ka gabatar da kuma tattauna (amma kar ka kunna) bidiyon nan Ka Tuna da Mutuwar Yesu. (th darasi na 11)
RAYUWAR KIRISTA
Za A Soma Gayyatar Mutane Zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu a Ranar 14 ga Maris: (minti 8) Tattaunawa. A ba kowa takardar gayyatar, sai ka yi bayani a kai. Ku kalli bidiyon yadda za a rarraba gayyatar, sai ku tattauna shi. Ka faɗi tsarin da ikilisiyarku za ta bi wajen gayyatar mutane a duk yankin.
“Su Wa Zan Gayyata?”: (minti 7) Tattaunawa.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) ia babi na 4 sakin layi na 1-15 da akwatin da ke shafi na 39
Kammalawa (minti 3 ko ƙasa da hakan)
Waƙa ta 9 da Addu’a