Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Su Wa Zan Gayyata?

Su Wa Zan Gayyata?

A kowace shekara, mukan yi ƙoƙari don mu gayyaci mutane zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Da yawa daga cikin waɗanda muke gayyata ba mu waye su ba. Yana da kyau mu gayyaci mutane da muka waye su ma. A yawancin lokaci, idan muka gayyaci waɗanda muka sani, zai musu sauƙi su halarci taron. (yb08-E 11 sakin layi na 3; 14 sakin layi na 1) Su waye ne za mu iya gayyata?

  • ’Yan’uwanmu

  • Abokan aikinmu ko na makaranta

  • Maƙwabtanmu

  • Ɗalibanmu na yanzu da na dā

Ban da haka ma, dattawa za su iya gayyatar ’yan’uwa da suka daina zuwa wa’azi. Idan kuma ’yan’uwa da abokanka ba sa zama a unguwar da kake fa? Ka shiga shafin farko a dandalin jw.org/⁠ha, sai ka danna GAME DA MU da ke saman shafin. Bayan haka, sai ka danna “Taron Tunawa da Mutuwar Yesu” don ka san lokaci da kuma inda za a yi taron a yankin da suke. Yayin da kake shirya Taron Tunawa da Mutuwar Yesu na wannan shekarar, ka yi tunani a kan waɗanda za ka gayyata, sa’an nan ka gayyace su.