16-22 ga Maris
FARAWA 25-26
Waƙa ta 18 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 1)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Isuwa Ya Sayar da Matsayinsa na Ɗan Fari”: (minti 10)
Fa 25:27, 28—Halin ’yan biyun nan Isuwa da Yakub da kuma aikin da suke yi sun bambanta (mwbr20.03-HA an ɗauko daga it-1 1242)
Fa 25:29, 30—Yunwa da gajiya sun sa Isuwa ya tsai da mummunar shawara
Fa 25:31-34—Isuwa bai ga muhimmancin matsayinsa na ɗan fari ba shi ya sa ya sayar da shi a bakin jar miya (w19.02 16 sakin layi na 11; mwbr20.03-HA an ɗauko daga it-1 835)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 10)
Fa 25:31-34—Me ya sa ayoyin nan ba su nuna cewa waɗanda Almasihu ya fito daga zuriyarsu ’ya’yan fari ne kawai ba? (Ibr 12:16; w17.12 15 sakin layi na 5-7)
Fa 26:7—Me ya sa Ishaku ya ce matarsa ’yar’uwarsa ce? (mwbr20.03-HA an ɗauko daga it-2 245 sakin layi na 6)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu game da Jehobah Allah da wa’azi da dai sauransu?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Fa 26:1-18 (th darasi na 5)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Bidiyon Komawa Ziyara ta Farko: (minti 5) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon sai ku tattauna tambayoyi na gaba: Ta yaya za mu guji kunyatar da mutane idan sun ba da amsar da ba daidai ba? Ta yaya mai shelan ya yi bayani a kan Matiyu 20:28?
Komawa Ziyara ta Farko: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Ka bi bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. (th darasi na 3)
Komawa Ziyara ta Farko: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Ka bi bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Sai ka ba wa mutumin littafin nan Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki? (th darasi na 15)
RAYUWAR KIRISTA
Ku Nuna Bidiyo Sa’ad da Kuke Nazari da Ƙasidar Nan Albishiri Daga Allah!: (minti 15) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon nan Wane Yanayi Ne Matattu Suke Ciki? da kuma Me Ya Sa Allah Ya Ƙyale Mutane Su Sha Wahala? Bayan kun kalli kowanne bidiyo, sai ku tattauna tambayoyin nan: Yaya za ka yi amfani da bidiyon nan sa’ad da kake nazari da ƙasidar nan Albishiri Daga Allah! (mwb19.03 7) Wane abu ka gani a bidiyon da zai taimaka maka sa’ad da kake koyarwa? Ka tuna ma ’yan’uwa cewa ƙasidar wadda take dandalinmu tana ɗauke da bidiyon da ya dace su nuna.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) ia babi na 4 sakin layi na 16-31 da Taƙaitawa da ke shafi na 41
Kammalawa (minti 3 ko ƙasa da hakan)
Waƙa ta 107 da Addu’a