Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | FARAWA 27-28

Yakub Ya Sami Albarkar da Ta Dace da Shi

Yakub Ya Sami Albarkar da Ta Dace da Shi

27:6-10, 18, 19, 27-29

Sa’ad da Ishaku ya albarkaci Yakub, yana yin annabci ne.

  • 27:28​—Jehobah ya ba wa zuriyar Yakub “ƙasa mai amfani.”​—M.Sh 26:15

  • 27:29​—Isra’ilawa (zuriyar Yakub) sun fi Edomawa (zuriyar Isuwa) ƙarfi sosai.​—Fa 25:23; 2Sam 8:14

  • 27:29​—Edomawa sun tsāne Isra’ilawa sosai kuma hakan ya sa an la’anta su kuma daga baya an halaka su gabaki ɗaya.​—Eze 25:​12-14