Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Yadda Za Mu Yi Wa Makafi Wa’azi

Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Yadda Za Mu Yi Wa Makafi Wa’azi

MUHIMMANCINSA: Makafi da yawa ba sa yawan son tattaunawa da waɗanda ba su sani ba. Saboda haka, muna bukatar basira sosai kafin mu iya yi musu wa’azi. Jehobah ya damu da makafi. (L.Fi 19:14) Za mu yi koyi da Jehobah idan muna iya ƙoƙarinmu mu taimaka wa makafi su soma bauta wa Jehobah.

YADDA ZA MU YI HAKAN:

  • “Ku nemi” makafi. (Mt 10:11) Ka san wasu da suke da makaho a iyalinsu? A yankinku akwai makaranta ko asibitin makafi da za su so littattafanmu na makafi?

  • Ku nuna kun damu da su. Idan kuka nuna cewa kun damu da makahon, zai iya sakewa da ku har ya ji wa’azinku. Ka yi ƙoƙari ka soma tattauna batun da zai ja hankalin makahon

  • Ku ba wa makafi abin da zai taimaka musu su san Jehobah. Ƙungiyarmu ta wallafa littattafai da sauti da yawa da za su taimaka wa makafi da waɗanda ba su gani sosai. Ka tambayi makahon yadda yake so ka koyar da shi. Mai kula da hidima ya tabbata cewa mai kula da littattafai ya yi odar littattafan da suka yi daidai da yanayin makafi a yankinsu