15-21 ga Maris
LITTAFIN ƘIDAYA 11-12
Waƙa ta 46 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 1)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Dalilin da Ya Sa Ya Dace Mu Guji Yin Gunaguni”: (minti 10)
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah: (minti 10)
L.Ƙi 11:7, 8—Ta yaya ɗanɗanon manna da yadda yake suka nuna cewa Jehobah mai alheri ne? (mwbr21.03-HA an ɗauko daga it-2 309)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu game da Jehobah da wa’azi da dai sauransu?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4) L.Ƙi 11:1-15 (th darasi na 2)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Gayyata Zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu: (minti 3) Ka soma da bin bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Bayan da maigidan ya nuna cewa yana son wa’azin, ka gabatar da kuma tattauna (amma kar ka kunna) bidiyon nan Ka Tuna da Mutuwar Yesu. (th darasi na 11)
Komawa Ziyara: (minti 3) Ka ziyarci mutumin da ya so wa’azinmu kuma ya karɓi takardar gayyata na Taron Tunawa da Mutuwar Yesu. (th darasi na 4)
Komawa Ziyara: (minti 5) Bayan an gama Taron Tunawa da Mutuwar Yesu, ka soma tattaunawa da wani da ya halarci taron kuma ka amsa tambayar da ya yi game da taron. (th darasi na 2)
RAYUWAR KIRISTA
“Kana Yin Shiri don Taron Tunawa da Mutuwar Yesu?”: (minti 15) Tattaunawa. Ka sanar da shirye-shiryen da ake yi game da Taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Ku kalli bidiyon nan Yadda Ake Yin Gurasar Jibin Maraice na Ubangiji.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lfb darasi na 18 da 19
Kammalawa (minti 3)
Waƙa ta 70 da Addu’a