Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

KA YI WA’AZI DA KWAZO | YADDA ZA KA DAƊA JIN DAƊIN WA’AZI

Yin Amfani da Kalmar Allah

Yin Amfani da Kalmar Allah

Kalmar Allah tana da iko sosai! (Ibr 4:12) Tana ma iya ratsa zuciyar waɗanda ba su san Allah ba. (1Ta 1:9; 2:13) Muna farin ciki sosai idan mutane suka ji daɗin wani abin da muka nuna musu daga Littafi Mai Tsarki.

KU KALLI BIDIYON NAN ZA KU JI DAƊIN ALMAJIRTARWA IDAN KUN INGANTA YADDA KUKE WA’AZI​—KU RIƘA AMFANI DA KALMAR ALLAH, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Ta yaya Anita ta yi amfani da Kalmar Allah don ta taimaka wa Rose ta ga muhimmancin bincika Kalmar Allah?

  • Ta yaya Anita ta sa Kalmar Allah ta ratsa zuciyar Rose ta wajen sa ta ta karanta nassin da babbar murya kuma ta ambata wani furuci a ayar da ya goyi bayan batun da suke tattaunawa?

  • Mene ne ya nuna cewa nassin ya ratsa zuciyar Rose, kuma ta yaya hakan ya shafi Anita?