Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

KA YI WA’AZI DA KWAZO | YADDA ZA KA DAƊA JIN DAƊIN WA’AZI

Yin Tambayoyi

Yin Tambayoyi

Jehobah, “Allah mai farin ciki” yana so mu ji daɗin wa’azi. (1Ti 1:​11, New World Translation) Za mu daɗa jin daɗin hidimarmu idan muka kyautata yadda muke wa’azi. Yin tambayoyi zai sa mutane su so saƙonmu kuma hakan hanya ce mai kyau na soma tattaunawa da mutane. Tambayoyi sukan sa mutane su yi tunani a kan batutuwa. (Mt 22:​41-45) Idan muka yi tambayoyi kuma muka saurara da kyau, yana kamar muna gaya ma ɗalibinmu cewa, ‘Kana da muhimmanci a gare ni.’ (Yaƙ 1:19) Amsar da mutumin ya bayar za ta taimaka mana mu san batun da za mu tattauna da shi.

KU KALLI BIDIYON NAN ZA KU JI DAƊIN ALMAJIRTARWA IDAN KUN INGANTA YADDA KUKE WA’AZI​—KU RIƘA YIN TAMBAYOYI, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Waɗanne halaye masu kyau ne Rose ta nuna?

  • Ta yaya Anita ta nuna cewa ta damu da Rose?

  • Ta yaya Anita ta yi tambayoyi don ta ƙara jan hankalin Rose ga wa’azinmu?

  • Ta yaya Anita ta yi amfani da tambayoyi don ta sa Rose ta yi tunani kuma ta fahimci batun?