Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ka Zaɓi Abokan Kirki

Ka Zaɓi Abokan Kirki

Abin da ya faru da Isra’ilawa a filayen Mowab gargaɗi ne ga Kiristoci a yau. (1Ko 10:​6, 8, 11) Isra’ilawa sun soma tarayya da matan Mowab masu lalata da bautar gumaka kuma hakan ya sa suka yaudare su su yi zunubi. Sakamakon zunubin da suka yi ya yi muni ba kaɗan ba. (L.Ƙi 25:9) A yau ma, muna da abokan aiki da abokan makaranta da maƙwabta da dangi da dai wasu da ba sa bauta wa Jehobah. Me za mu iya koya daga wannan labari game da munanan abubuwan da za mu iya fuskanta idan mun yi tarayya da mutanen da ba sa bauta wa Jehobah?

KU KALLI BIDIYON NAN DARUSSA DAGA MUNANAN MISALAN MUTANEN DĀ​—TAƘAITAWA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Wane ra’ayin da bai dace ba ne Zimri da wasu suka so su cusa wa Jamin?

  • Ta yaya Finehas ya taimaka wa Jamin ya daidaita ra’ayinsa?

  • Mene ne bambancin yin alheri ga wanda ba ya bauta wa Jehobah da kuma zama abokinsa?

  • Me ya sa ya kamata mu mai da hankali wajen zaɓan abokai ko a ƙungiyar Jehobah ma?

  • Me ya sa ya kamata mu guji rukunonin sada zumunta na mutanen da ba mu san su ba?