Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Ku Guji Girman Kai da Iya Yi

Ku Guji Girman Kai da Iya Yi

Kora ya ƙi bin tsarin da Jehobah ya kafa domin shi mai girman kai ne da iya yi (L.Ƙi 16:​1-3; w11 9/15 27 sakin layi na 12)

Kora Ba-lawi ne da ake darajawa sosai kuma yana yin ayyuka masu muhimmanci a bautar Jehobah (L.Ƙi 16:​8-10; w11 9/15 27 sakin layi na 11)

Tunani mara kyau da Kora ya yi ya jawo mummunar sakamako (L.Ƙi 16:​32, 35)

Kada mu soma nuna girman kai ko iya yi saboda abubuwan da muka cim ma a ƙungiyar Jehobah. Idan mun daɗe muna bauta ma Jehobah ko kuma muna yin ayyuka masu muhimmanci a ƙungiyar Jehobah, yana da muhimmanci mu riƙa kasancewa da tawali’u sosai.