Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ku Guji Koyi da Marasa Aminci

Ku Guji Koyi da Marasa Aminci

Kora da Datan da kuma Abiram sun nuna rashin aminci ga Jehobah don sun ƙi bin tsarin da Jehobah ya kafa. Jehobah ya hallaka su da waɗanda suka goyi bayansu. (L.Ƙi 16:​26, 27, 31-33) Wane irin yanayi ne zai iya gwada amincinmu ga Jehobah? Waɗanne labaran Littafi Mai Tsarki ne za su taimaka mana mu guji yin koyi da marasa aminci?

KU KALLI BIDIYON NAN KADA KU YI KOYI DA MARASA AMINCI, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Wane gwajin bangaskiya ne Nadia ta fuskanta, kuma wane labari mara kyau ne ya taimaka mata ta nuna aminci?

  • Wane abu ne ya ɓata ma wani ɗan’uwa rai, kuma wane labari mara kyau ne ya taimaka masa ya nuna aminci?

  • Wane gwajin bangaskiya ne Terrance ya fuskanta, kuma wane labari mara kyau ne ya taimaka masa ya nuna aminci?

  • Wane gwajin bangaskiya ne wani ɗan’uwa ya fuskanta a makaranta, kuma wane labari mara kyau ne ya taimaka masa ya nuna aminci?