8-14 ga Maris
LITTAFIN ƘIDAYA 9-10
Waƙa ta 31 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 1)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Yadda Jehobah Yake Ja-gorar Mutanensa”: (minti 10)
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah: (minti 10)
L.Ƙi 9:13—Wane darasi ne Kiristoci za su koya daga wannan umurni da aka ba wa Isra’ilawa? (mwbr21.03-HA an ɗauko daga it-1 199 sakin layi na 3)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu game da Jehobah da wa’azi da dai sauransu?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4) L.Ƙi 10:17-36 (th darasi na 5)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Gayyata Zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu: (minti 3) Ka soma da bin bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Bayan maigidan ya nuna cewa yana son wa’azin, ka gabatar da kuma tattauna (amma kar ka kunna) bidiyon nan Ka Tuna da Mutuwar Yesu. (th darasi na 11)
Komawa Ziyara: (minti 3) Ka gayyaci abokin aikinka ko abokin makarantarka da ka taɓa masa wa’azi zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu. (th darasi na 2)
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 5) bhs 214, ƙarin bayani na 16—Ka gayyaci ɗalibinka zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu kuma ka bayyana masa daga Littafi Mai Tsarki dalilin da ya sa bai kamata ya ci gurasa ko kuma ya sha ruwan inabin ba. (th darasi na 17)
RAYUWAR KIRISTA
Canje-canje da Aka Yi a Bethel Sun Taimaka a Wa’azi: (minti 10) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon. Bayan haka, sai ku amsa waɗannan tambayoyin: Wace sanarwa ce aka yi a taron shekara-shekara na 2015, kuma waɗanne dalilai biyu ne suka sa aka yi canje-canjen? Waɗanne canje-canje aka yi a Bethel, kuma wane amfani aka samu? Ta yaya sanarwar ta shafi sabon ofishinmu na Birtaniya? Ta yaya waɗannan canje-canje suka nuna cewa Jehobah ne yake ja-gorar ƙungiyarmu?
Dalilin da Ya Sa Muka Je Bethel: (minti 5) Ku kalli bidiyon.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lfb darasi na 17
Kammalawa (minti 3)
Waƙa ta 12 da Addu’a