RAYUWAR KIRISTA
Hanyoyi Uku da Za Mu Dogara ga Jehobah
Dauda ya yi nasara a kan Goliyat don ya dogara ga Jehobah. (1Sam 17:45) Jehobah yana so ya taimaka wa bayinsa. (2Tar 16:9) Ta yaya za mu dogara ga Jehobah maimakon mu dogara ga kanmu? Ga hanyoyi uku:
-
Ku riƙa addu’a a kai a kai. Bai kamata mu riƙa addu’a kawai don neman gafarar zunubanmu ba, amma don mu sami ƙarfin jimre jarrabawa. (Mt 6:12, 13) Mu riƙa addu’a don neman ja-gorancin Jehobah da hikimarsa kafin mu yanke shawarwari. Bai kamata mu riƙa neman albarkarsa kawai bayan mun yanke shawara ba.—Yak 1:5
-
Ku tsara yadda za ku riƙa karanta Littafi Mai Tsarki da kuma nazarinsa. Ku dinga karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana. (Za 1:2) Ku riƙa tunani game da misalan bayin Allah da aka ambata a Littafi Mai Tsarki, kuma ku yi amfani da darussan da kuka koya. (Yak 1:23-25) Ku riƙa shiri don wa’azi maimakon ku riƙa amfani da abin da kuka sani a dā kawai. Ku riƙa shirya abubuwan da za a yi nazarinsu a taro don ku amfana sosai
-
Ku riƙa yin abin da ƙungiyar Jehobah ta gaya muku. Ku yi ƙoƙari ku san kuma ku bi umurnan da ƙungiyar Jehobah take bayarwa kwanan nan. (L.Ƙi 9:17) Ku bi umurnan da dattawa suke ba ku.—Ibr 13:17
KU KALLI BIDIYON NAN KADA KU JI TSORON TSANANTAWA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
• Mene ne ya sa ’yan’uwan tsoro?
• Me ya taimaka musu su daina jin tsoro?