Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

KA YI WA’AZI DA KWAZO | YADDA ZA KA DAƊA JIN DAƊIN WA’AZI

Ka Taimaka wa Dalibanka Su Daina Halayen da Jehobah Ba Ya So

Ka Taimaka wa Dalibanka Su Daina Halayen da Jehobah Ba Ya So

Waɗanda suke da ɗabi’u masu kyau ne kawai, za su more dangantaka na kud da kud da Jehobah. (1Bi 1:14-16) Idan ɗalibanmu suka daina halaye marasa kyau, iyalinsu za su amfana, za su kasance da ƙoshin lafiya kuma ba za su riƙa kashe kuɗi a banza ba.

Ka bayyana musu ƙa’idodin Jehobah game da ɗabi’a, da dalilin da ya sa za su bi ƙa’idodin da kuma amfaninsu. Ka mai da hankali wajen taimaka wa ɗalibanka su canja ra’ayinsu, ta hakan za su yi abin da Jehobah yake so. (Afi 4:22-24) Ka tabbatar musu cewa Jehobah zai taimaka musu su daina halin da ya zama musu jiki. (Fib 4:13) Ka koya musu yadda za su yi addu’a sa’ad da suka fuskanci jarabar yin zunubi. Ka taimaka musu su san yanayoyin da za su iya jefa su cikin matsala kuma su guje su. Ka ƙarfafa su su riƙa yin abubuwan da za su amfane su maimakon abubuwa marasa kyau. Za ka yi farin ciki sa’ad da ka ga yadda Jehobah yake taimaka wa ɗalibanka su yi canje-canje a rayuwarsu.

KU KALLI BIDIYON NAN KU TAIMAKA WA ƊALIBANKU SU DAINA HALAYEN DA JEHOBAH BA YA SO, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Ta yaya dattawa da Anita suka nuna cewa sun amince da Rose?

  • Ta yaya Anita ta ƙara taimaka wa Rose?

  • Ta yaya Rose ta nemi taimakon Jehobah?