Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Dukan Jarrabobi Suna da Ranar da Za Su Ƙare

Dukan Jarrabobi Suna da Ranar da Za Su Ƙare

Jarrabawa takan sa mu sanyin gwiwa, musamman idan sun ƙi ci sun ƙi cinyewa. Dauda ya san cewa wata rana Sarki Saul zai daina taƙura masa kuma zai zama sarki yadda Jehobah ya yi masa alkawari. (1Sam 16:13) Dauda ya kasance da bangaskiya, hakan ya taimaka masa ya dogara ga Jehobah cewa zai canja yanayinsa.

Sa’ad da muke fuskantar jarrabawa, basira da hikima da kuma yin tunanin kirki za su iya taimaka mana mu canja yanayinmu. (1Sam 21:12-14; K. Ma 1:4) Amma, za mu iya ci gaba da fuskantar wasu matsaloli ko da mun yi iya ƙoƙarinmu don mu bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. A irin wannan yanayin, wajibi ne mu kasance da haƙuri kuma mu dogara ga Jehobah. Nan ba da daɗewa ba, zai kawar da dukan matsalolinmu kuma ya “share . . . dukan hawaye” daga idanunmu. (R. Yar 21:4) Ko mun sami sauƙi domin Jehobah ya taimaka mana ko kuma don wasu dalilai, mun sani cewa: Kowace jarrabawa tana da ƙarshe. Kuma hakan yana ba mu ƙarfin gwiwa.

KU KALLI BIDIYON NAN NUNA HAƊIN KAI A DUNIYA CIKE DA NUNA WARIYA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Waɗanne matsaloli ne wasu Kiristoci suka fuskanci a kudancin Amirka?

  • Ta yaya suka nuna haƙuri da ƙauna?

  • Ta yaya suka ci gaba da mai da hankali ga abin da ya fi muhimmanci?—Fib 1:10