RAYUWAR KIRISTA
Karatun Littafi Mai Tsarki Kowace Rana da Neman Hikima
Hikimar Allah tana da daraja kamar dukiyar da take a ɓoye. (K. Ma 2:1-6) Hikima tana taimaka mana mu zama masu basira kuma mu riƙa tsai da shawarwari masu kyau. Ƙari ga haka, tana kāre mu. Saboda haka, hikima “muhimmin abu” ne. (K. Ma 4:5-7) Muna bukatar mu ƙoƙarta sosai don mu iya samun abubuwa masu daraja da suke Kalmar Allah. Za mu iya somawa ta wurin karanta Kalmar Allah “dare da rana.” (Yos 1:8) Ku lura da waɗansu shawarwarin da za su taimaka mana mu riƙa karanta Kalmar Allah a kai a kai kuma mu ji daɗin sa.
KU KALLI BIDIYON NAN YADDA WASU MATASA SUKA KYAUTATA KARATUN KALMAR ALLAH, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
Me ya sa yake yi ma waɗannan matasan wuya su riƙa karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana, amma me ya taimaka musu?
-
Melanie
-
Samuel
-
Celine
-
Raphaello
TSARIN DA ZAN RIƘA BI A KARATUN LITTAFI MAI TSARKI: