RAYUWAR KIRISTA
Yadda Za a Yi Amfani da Bidiyoyin Nazari
Muna da bidiyoyi huɗu da muke amfani da su saꞌad da muke waꞌazi. Me ya sa aka shirya kowannensu?
-
Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki?—Cikakken Bidiyon, wannan bidiyo ne da aka shirya don a taimaka wa mutane su so Littafi Mai Tsarki ko da wane addinni ne suke bi. Bidiyon ya ƙarfafa mutane su nemi amsoshin tambayoyi game da rayuwa a cikin Littafi Mai Tsarki kuma ya ɗan nuna wasu amsoshi da za a samu a ciki. Ya bayyana yadda mutum zai nemi a riƙa nazarin Littafi Mai Tsarki da shi.
-
Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki? (gajeren bidiyon), wannan bidiyon yana kama da cikakken bidiyon, amma tsawonsa kashi uku ne na cikakken bidiyon. Wannan zai fi dacewa da yankunan da mutanen ba su da lokaci.
-
Yaya Ake Gudanar da Nazarin Littafi Mai Tsarki? bidiyo ne da aka shirya don a sa mutane su so nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ya amsa wasu tambayoyin da mutane suke yi game da nazari, da kuma yadda mutum zai nemi a riƙa nazarin Littafi Mai Tsarki da shi.
-
Maraba da Zuwa Nazarin Littafi Mai Tsarki, bidiyo ne da aka shirya don a nuna wa ɗalibai. Ko da yake an gabatar da bidiyon a shafi na biyu na littafin Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! za a iya nuna wa ɗalibi saꞌad da aka soma tattauna ƙasidar Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! da shi. Bidiyon ya bayyana abin da ke cikin littafin da abin da ɗalibin zai koya saꞌad da yake nazarin.
Ko da yake an shirya kowane bidiyon don manufa dabam-dabam, za mu iya nuna wa mutane ko kuma mu tura musu kowannensu saꞌad da yin hakan ya dace. Ya kamata masu shela su san bayanai cikin bidiyon da kyau kuma su yi amfani da su sosai a waꞌazi.