20-26 ga Maris
2 TARIHI 1-4
Waƙa ta 41 da Adduꞌa
Gabatarwar Taro (minti 1)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Sarki Sulemanu Ya Tsai da Shawarar da Ba Ta Dace Ba”: (minti 10)
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah: (minti 10)
2Tar 1:11, 12—Mene ne wannan labarin ya koya mana game da yadda za mu riƙa yin adduꞌoꞌin kanmu? (w05 12/1 29 sakin layi na 6)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu game da Jehobah da waꞌazi da dai sauransu?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4) 2Tar 4:7-22 (th darasi na 10)
KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO
Gayyata Zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu: (minti 3) Ka gayyaci abokin aikinka ko abokin makaranta ko kuma danginka. (th darasi na 2)
Komawa Ziyara: (minti 4) Ka ziyarci mutumin da ya so waꞌazinmu kuma ya karɓi takardar gayyata na Taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Ka bayyana masa yadda muke yin nazari da mutane kyauta, kuma ka ba shi ƙasidar Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! Ka gabatar kuma ku tattauna (amma kar ka kunna) bidiyon nan Yaya Ake Gudanar da Nazarin Littafi Mai Tsarki? (th darasi na 17)
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 5) lff darasi na 09 batu na 5 (th darasi na 9)
RAYUWAR KIRISTA
Za Ka Yi Shiri don Rana Mafi Muhimmanci a Wannan Shekarar?: (minti 15) Jawabi da bidiyo. Mai kula da hidima ne zai ba da wannan jawabin. Ka bayyana ci gaba da ake samu a yankinku game da waꞌazi na musamman da ake yi don gayyatar mutane zuwa taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Ka gana da waɗanda suke da labarai masu daɗi saꞌad da suka yi wannan waꞌazin. Ka nuna tsarin karatun Littafi Mai Tsarki don taron da ke shafuffuka na 8 da 9, ka ƙarfafa dukan ꞌyanꞌuwa su shirya zukatansu don taron. (Ezr 7:10) Ka tattauna yadda za mu marabci baƙinmu a ranar taron. (Ro 15:7; mwb16.03 2) Ku kalli bidiyon Yadda Ake Yin Gurasar Jibin Maraice na Ubangiji.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lff darasi na 41 batu na 1-4
Kammalawa (minti 3)
Waƙa ta 135 da Adduꞌa