DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
A Wane Lokaci Ne Za Mu Dogara Ga Jehobah?
Asa ya dogara ga Jehobah don ya taimaka masa ya yi nasara a kan sojoji da yawa (2Tar 14:9-12; w21.03 5 sakin layi na 12)
Daga baya Asa ya nemi taimakon mutanen Suriya don su taimaka masa ya yi nasara a kan sojoji da ba su da yawa (2Tar 16:1-3; w21.03 5 sakin layi na 13)
Jehobah ya yi fushi da Asa domin bai ci gaba da neman taimakonsa ba (2Tar 16:7-9)
Yana da sauƙi mu dogara ga Jehobah saꞌad da muke so mu yanke shawarwari masu muhimmanci. Amma me za mu yi a wasu lokutan kuma fa? Zai dace mu riƙa neman taimakon Jehobah a kowane lokaci.—K. Ma 3:5, 6; w21.03 6 sakin layi na 14.