RAYUWAR KIRISTA
Yadda Za Mu Taimaka Bayan Wani Balaꞌi
Balaꞌoꞌi suna ƙaruwa a kwanakin nan. Idan balaꞌi ya faru, ya kamata a tsara yadda za a ba da agaji da kyau. Saboda haka, Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta shirya a kafa Sashen Kula da Agaji a kowane reshen ofishinmu.
Idan ꞌyanꞌuwan da suke aiki a wannan sashen suka samu labari cewa wani balaꞌi ya faru, za su tuntuɓi dattawa da suke wurin nan da nan don su san taimakon da masu shela suke bukata. Idan ɓarnar ta fi ƙarfin ꞌyanꞌuwa da ke yankin, ꞌyanꞌuwa da ke reshen ofishi za su tura ꞌyanꞌuwa da suka ƙware a wannan fanni don su ja-goranci aikin ba da agajin. ꞌYanꞌuwan suna iya neman mutanen da za su taimaka a aikin ko kuma su nemi a ba da gudummawar wasu kaya. Ban da haka, suna iya sayan wasu kayayyaki a yankin kuma su rarraba.
Yin hakan yana da amfani ainun domin zai hana mutane da yawa su yi abu ɗaya, ko kashe kuɗi a banza, ko kuma ɓata kayayyakin aiki. Hakan zai iya faruwa idan aka bar ꞌyanꞌuwa su taimaka yadda suke so.
ꞌYanꞌuwa da reshen ofishin suka ba aikin za su san yawan kuɗi da kuma mutanen da za a bukaci don yin aikin agajin. Za su kuma iya neman taimakon maꞌaikatan gwamnati a yankin, da za su iya taimaka wajen sa aikin ba da agajin ya yi sauri. Saboda haka, kada mutane su karɓi kuɗi ko tura kayan agaji ko kuma su je wurin da balaꞌin ya faru, sai dai ko an gaya musu su yi hakan.
Duk da haka, idan balaꞌi ya faru, mukan so mu taimaka. (Ibr 13:16) Muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu sosai, don haka mene ne za mu iya yi? Abin da ya fi muhimmanci da za mu yi shi ne yin adduꞌa a madadin mutanen da balaꞌin ya shafa da kuma waɗanda suke ba da agaji. Ƙari ga haka, muna iya ba da gudummawar kuɗi ta wurin tallafa wa ayyukan da ake yi a faɗin duniya. Ta wurin bin ja-gorancin Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu, ꞌyanꞌuwa da ke reshen ofisoshi za su fi sanin wurin da za a fi taimaka wa mutane. Amma idan muna so mu taimaka da aikin, za mu iya cika fom Local Design/Construction Volunteer Application (DC-50).
KU KALLI BIDIYON NAN, BALAꞌIN AMBALIYAR RUWA A BRAZIL, SAI KU AMSA TAMBAYA NA GABA:
Mene ne ya burge ka game da yadda Shaidun Jehobah suka ba da agaji bayan an yi ambaliyar ruwa a Brazil a 2020?