Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

10-16 ga Maris

KARIN MAGANA 4

10-16 ga Maris

Waƙa ta 36 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Masu tsaro da masu gadi suna rufe kofofin birnin da sauri don kar magabta su shiga

1. Ku ‘Kiyaye Zuciyarku’

(minti 10)

Kalmar nan “zuciya” tana nufin halin mutum ko abin da yake ciki-cikin zuciyar mutum (Za 51:6; w19.01 shafi na 15 sakin layi na 4)

Burinmu shi ne mu kāre tunaninmu da halinmu daga abubuwan da za su iya lalace su (K. Ma 4:23a; w19.01 shafi na 17 sakin layi na 10-11; shafi na 18 sakin layi na 14; ka duba hoton shafin farko)

Samun rai na har abada ya dangana ga abin da ke cikin zuciyarmu (K. Ma 4:23b; w12 7/1 shafi na 32 sakin layi na 2)

2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah

(minti 10)

  • K. Ma 4:18—Ta yaya ayar nan take taimaka mana mu san yadda mutum yake kusantar Jehobah? (w21.08 shafi na 8 sakin layi na 4)

  • A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?

3. Karatun Littafi Mai Tsarki

(minti 4) K. Ma 4:1-18 (th darasi na 12)

KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO

4. Fara Magana da Mutane

(minti 3)WAꞌAZI GIDA-GIDA. Mutumin ya ce zai zo taron bayan ka ba shi takardar gayyata na taron Tunawa da Mutuwar Yesu. (lmd darasi na 1 batu na 5)

5. Fara Magana da Mutane

(minti 4) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka gayyaci wani da ka sani zuwa taron Tunawa da Mutuwar Yesu. (lmd darasi na 2 batu na 3)

6. Ka Bayyana Imaninka

(minti 5) Gwaji. ijwfq talifi na 19—Jigo: Me Ya Sa Ba Ku Yin Bikin Ista? (lmd darasi na 3 batu na 4)

RAYUWAR KIRISTA

Waƙa ta 16

7. Abubuwan da Ƙungiyarmu Ta Cim Ma na Watan Maris

(minti 10) Ku kalli BIDIYON.

8. Za A Soma Gayyatar Mutane Zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu Ran Asabar 15 ga Maris

(minti 5) Jawabi da mai kula da hidima zai yi. Ka gaya wa ꞌyanꞌuwa shirye-shiryen da aka yi don waꞌazi na musamman da jawabi na musamman da kuma taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Ka ƙarfafa ꞌyanꞌuwa su ƙara ƙwazo a waꞌazi a watan Maris da Afrilu.

9. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya

Kammalawa (minti 3) | Waƙa ta 76 da Adduꞌa