Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

17-23 ga Maris

KARIN MAGANA 5

17-23 ga Maris

Waƙa ta 122 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

1. Ku Guji Halin Lalata

(minti 10)

Jarabar yin lalata na da ƙarfi sosai (K. Ma 5:3; w00-E 7/15 29 sakin layi na 1)

Lalata takan jawo baƙin ciki (K. Ma 5:4, 5; w23.06 22-23 sakin layi na 9-10)

Ku guji halin lalata (K. Ma 5:8; w15 6/15 15-16 sakin layi na 8-10)

Wata ꞌyarꞌuwa ta ƙi ta ba wani yaro lambar wayarta

2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah

(minti 10)

  • K. Ma 5:18, 19—Mene ne raꞌayin Jehobah game da jimaꞌi? (lff darasi na 41 batu na 1)

  • A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?

3. Karatun Littafi Mai Tsarki

(minti 4) K. Ma 5:1-23 (th darasi na 5)

KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO

4. Fara Magana da Mutane

(minti 3) WAꞌAZI A INDA JAMAꞌA SUKE. Ka gayyaci wani da ba Kirista ba zuwa taron Tunawa da Mutuwar Yesu, kuma ka yi amfani da dandalin jw.org/ha ka nuna masa wurin da za a yi taron kusa da yankinsu. (lmd darasi na 6 batu na 4)

5. Komawa Ziyara

(minti 4) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Kwanan baya da ka ziyarci mutumin, ya karɓi gayyata na taron Tunawa da Mutuwar Yesu kuma ya ce zai zo. (lmd darasi na 9 batu na 5)

6. Almajirtarwa

(minti 5) Ku tattauna taƙaitawa da bita da kuma maƙasudi da ke lff darasi na 16. Idan daliɓin ya tambaye ka ko Yesu ya yi aure, ka nuna masa yadda zai yi bincike da kansa don ya sami amsar. (lmd darasi na 11 batu na 4)

RAYUWAR KIRISTA

Waƙa ta 121

7. Yadda Za Ku Guji Lalata Saꞌad da Kuke Fita Zance

(minti 15) Tattaunawa.

Fita zance zai iya nufin “yin duk wasu abubuwa da za su nuna cewa mutane biyu suna soyayya.” Za su iya yin abubuwan nan saꞌad da suke cikin jamaꞌa ko su kaɗai. Za su iya yin hakan a idon jamaꞌa ko a asirce ko ta waya ko kuma ta tura saƙonnin tes. Fita zance ba nishaɗi ba ne, amma abu ne da ake yi da zai kai ga yin aure. Waɗanne matakai ne waɗanda suke fita zance za su ɗauka don kada su yi lalata?—K. Ma 22:3.

Ku kalli BIDIYON Yadda Za Ka Yi Shirin Yin Aure—Kashi na 1: Shin, a Shirye Nake In Soma Fita Zance?—Taƙaitawa. Sai ka tambayi masu sauraro:

  • Me ya sa zai dace mutum ya shirya yin aure kafin ya soma fita zance? (K. Ma 13:12; Lu 14:28-30)

  • Yaya ka ga yadda iyayen nan suka taimaka wa ꞌyarsu?

Karanta Karin Magana 28:26. Sai ka tambayi masu sauraro:

  • Ta yaya waɗanda suke fita zance za su yi shiri tun da wuri don kada su kasance a yanayin da zai iya sa su yi lalata?

  • Me ya sa zai dace masu fita zance su tattauna tun da wuri abin da za su yi da abin da ba za su yi ba a batun da ya shafi riƙe hannu da sumba?

Karanta Afisawa 5:3, 4. Sai ka tambayi masu sauraro:

  • Me ya sa zai dace waɗanda suke fita zance su mai da hankali da irin hirar da suke yi ta waya ko a kafofin sada zumunta?

8. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya

Kammalawa (minti 3) | Waƙa ta 3 da Adduꞌa