21-27 ga Afrilu
KARIN MAGANA 10
Waƙa ta 76 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)
1. Ta Yaya Za Mu Sami Farin Ciki Na Gaske?
(minti 10)
Rayuwa mai maꞌana ta ƙunshi yin ƙwazo a waꞌazi (K. Ma 10:4, 5; w01-E 7/15 25 sakin layi na 1-3)
Kasancewa da adalci ya fi arziki daraja (K. Ma 10:15, 16; w01-E 9/15 24 sakin layi na 3-4)
Albarkar Jehobah ce take kawo farin ciki na gaske (K. Ma 10:22; it-1-E 340)
2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
(minti 10)
-
K. Ma 10:22—Ta yaya waɗanda suke duniya za su sami albarka daga Jehobah? (w20.08 shafi na 17 sakin layi na 12)
-
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?
3. Karatun Littafi Mai Tsarki
(minti 4) K. Ma 10:1-19 (th darasi na 10)
4. Fara Magana da Mutane
(minti 4) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Mutumin ya ce shi bai yi imani da Allah ba. (lmd darasi na 4 batu na 3)
5. Fara Magana da Mutane
(minti 4) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka tambayi mutumin ko zai so a yi nazari da shi. (lmd darasi na 4 batu na 4)
6. Komawa Ziyara
(minti 4) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka nuna ma mutumin yadda zai sami bayanin da zai so a dandalin jw.org/ha. (lmd darasi na 9 batu na 4)
Waƙa ta 111
7. Waɗanne Albarku Ne Suke Sa Bayin Jehobah Farin Ciki?
(minti 7) Tattaunawa.
Yadda Jehobah yake mana albarka a waɗannan kwanaki na ƙarshe ne yake taimaka mana mu bauta masa da farin ciki. (Za 4:3; K. Ma 10:22) Ku karanta nassosi na gaba. Sai ka tambayi ꞌyanꞌuwa yadda albarkun Jehobah suke sa mu yi farin ciki.
-
Ish 65:13
-
Lu 11:13
-
Yoh 13:35
Wasu ꞌyanꞌuwa sun faɗaɗa hidimarsu kuma suna moran albarku daga Jehobah.
Ku kalli BIDIYON Ku Zabi Rayuwar da Za Ta Ba Ku Kwanciyar Hankali! Sai ka tambayi masu sauraro:
-
Mene ne labarin Harley da Anjil da kuma Carlee ya koya maka?
8. Ƙarin Bayani na Sashen Zane-Zane da Gine-Gine na 2025
(minti 8) Jawabi. Ku kalli BIDIYON.
9. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya
(minti 30) w23.3 28-31 sakin layi na 11-19