28 ga Afrilu–4 ga Mayu
KARIN MAGANA 11
Waƙa ta 90 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)
1. Kada Ku Faɗi Abu Marar Kyau!
(minti 10)
Kada ku faɗi wani abu da zai ɓata sunan ‘maƙwabcinku’ (K. Ma 11:9; w02-E 5/15 26 sakin layi na 4)
Kada ku faɗi wani abin da zai iya ɓata zaman lafiya (K. Ma 11:11; w02-E 5/15 27 sakin layi na 2-3)
Kada ku yaɗa wani abu da aka gaya muku a asirce (K. Ma 11:12, 13; w20.03 21-22 sakin layi na 12-13)
DON BIMBINI: Ta yaya abin da Yesu ya faɗa a Luka 6:45 zai taimaka mana kada mu faɗi wani abu marar kyau?
2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
(minti 10)
-
K. Ma 11:17—Ta yaya za mu amfana idan muna nuna halin kirki? (w18.11 30 sakin layi na 4-6)
-
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?
3. Karatun Littafi Mai Tsarki
(minti 4) K. Ma 11:1-20 (th darasi na 5)
4. Fara Magana da Mutane
(minti 4) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka nemi dama ka gaya wa mutumin abin da ka koya a taronmu kwanan nan. (lmd darasi na 2 batu na 4)
5. Komawa Ziyara
(minti 4) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka nuna bidiyo daga cikin Kayan Aiki don Koyarwa. (lmd darasi na 8 batu na 3)
6. Almajirtarwa
(minti 4) WAꞌAZI A INDA JAMAꞌA SUKE. Ka nuna yadda muke gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki. (lmd darasi na 10 batu na 3)
Waƙa ta 157
7. Kada Ku Yi Amfani da Harshenku a Hanyar da Za Ta Ɓata Zaman Lafiya
(minti 15) Tattaunawa.
Da yake mu ajizai ne, a wasu lokuta za mu iya faɗan abubuwan da ba su dace ba. (Yak 3:8) Amma idan muka yi tunani a kan irin matsalar da za mu jawo wa kanmu idan muka faɗi wani abu marar kyau, hakan zai taimaka mana mu mai da hankali ga abin da muke faɗa. Ga wasu maganganu da za su iya sa a daina kasancewa da salama a ikilisiya:
-
Maganganun ɗaga kai. Wanda yake irin wannan furucin yana yabon kansa ne kuma hakan zai iya jawo gāsa da kuma hassada.—K. Ma 27:2
-
Maganganun Ruɗu. Wanda yake maganganun ruɗu ba wai yana yin ƙarya kai tsaye kawai ba, amma da gangan yake furuci don ya yaudari mutane. Ko da muna gani kamar ƙarya da muka yi a kan wani abu karami ne kawai, hakan zai iya ɓata sunanmu kuma ya sa mutane su daina yarda da mu.—M. Wa 10:1
-
Gulma. Mutum mai gulma yakan yi maganganu marasa amfani game da mutane da yadda suke rayuwarsu ko yaɗa abubuwan da ba su kamata ba. (1Ti 5:13) Hakan zai iya jawo saɓani da rashin zaman lafiya
-
Maganganun da za su sa mutane fushi. Mutane sukan yi zagi ko maganganun da ba su dace ba idan aka ɓata musu rai. (Afi 4:26) Hakan zai iya sa wanda aka masa maganar ya yi fushi.—K. Ma 29:22
Ku kalli BIDIYON “Ku Yar da” Duk Abin da Ke Bata Zaman Salama—Taƙaitawa. Sai ka tambayi masu sauraro:
-
Ta yaya furucinmu zai iya ɓata zaman salama a ikilisiya?
Don ku ga yadda aka sasanta matsalar, ku kalli bidiyon nan Ku ‘Nemi Salama da Dukan Zuciyarku.’
8. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya
(minti 30) w23.4 2-5 sakin layi na 1-12