3-9 ga Maris
KARIN MAGANA 3
Waƙa ta 8 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)
1. Ku Riƙa Dogara ga Jehobah
(minti 10)
Ku dogara ga Jehobah, kada ku dogara ga ganewarku (K. Ma 3:5; w11 11/15 shafi na 6 sakin layi na 2-3)
Ku dogara ga Jehobah ta wurin nema da kuma bin ja-gorancinsa (K. Ma 3:6; w03 9/1 shafi na 25 sakin layi na 22-23)
Kada ku ɗauka cewa kun san kome kuma ba za ku taɓa yin kuskure ba (K. Ma 3:7; w13 8/15 shafi na 13 sakin layi na 13)
KA TAMBAYI KANKA, ‘Shin, ina dogara ga Jehobah a duk abubuwan da nake yi a rayuwata?’
2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
(minti 10)
-
K. Ma 3:3—Ta yaya za mu ɗaura ƙauna da aminci a wuyarmu, kuma mu rubuta su a allon zuciyarmu? (w06 11/1 27 sakin layi na 3)
-
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?
3. Karatun Littafi Mai Tsarki
(minti 4) K. Ma 3:1-18 (th darasi na 12)
4. Fara Magana da Mutane
(minti 3) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Mutumin ya ba da wata hujja da aka saba bayarwa. (lmd darasi na 1 batu na 5)
5. Fara Magana da Mutane
(minti 4) WAꞌAZI A INDA JAMAꞌA SUKE. Ka gaya wa mutumin game da dandalin jw.org/ha kuma ka ba shi katin jw.org/ha. (lmd darasi na 3 batu na 3)
6. Jawabi
(minti 5) w11 3/15 shafi na 14 sakin layi na 7-10—Jigo: Ka Dogara ga Jehobah Idan Mutane Ba Sa So Su Ji Waꞌazi. (th darasi na 20)
Waƙa ta 124
7. Ku Nuna Cewa Kun Dogara ga Ƙungiyar Jehobah
(minti 15) Tattaunawa.
Ba zai yi wuya mu amince da ja-gorancin Kalmar Allah, wato Littafi Mai Tsarki ba. Amma idan ya zo ga bin umarni daga mutane ajizai da suke ja-goranci a ƙungiyar Jehobah, hakan zai iya zama da wuya musamman idan ba mu fahimci ko yarda da umarnin ba.
Karanta Malakai 2:7. Sai ka tambayi masu sauraro:
-
Me ya sa ba ma yin mamaki cewa Jehobah yana yin amfani da ꞌyanꞌuwa maza ajizai ya ja-goranci mutanensa?
Karanta Matiyu 24:45. Sai ka tambayi masu sauraro:
-
Me ya sa za mu iya yarda da ja-gorancin da muke samu daga ƙungiyar Jehobah?
Karanta Ibraniyawa 13:17. Sai ka tambayi masu sauraro:
-
Me ya sa zai dace mu bi ja-gorancin waɗanda Jehobah ya naɗa?
Ku kalli BIDIYON 2021 Karin Bayani na 9 Daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu—Taƙaitawa. Sai ka tambayi masu sauraro:
-
Ta yaya umurnan da muka samu a lokacin annobar korona ya ƙarfafa ka ka ƙara dogara ga ƙungiyar Jehobah?
8. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya
(minti 30) w23.2 20-22 sakin layi na 1-9