7-13 ga Afrilu
KARIN MAGANA 8
Waƙa ta 89 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)
1. Ku Kasa Kunne ga Mai Hikima
(minti 10)
Yesu wanda littafin Karin Magana ya kwatanta da hikima, Jehobah ne ya halicce shi, kuma shi ne “farkon halitta” (K. Ma 8:1, 4, 22; cf-E 131 sakin layi na 7)
Ba shakka, hikimar Yesu da ƙaunarsa ya daɗa ƙaruwa saꞌad da ya yi dubban shekaru yana aiki kusa da Jehobah (K. Ma 8:30, 31; cf-E 131-132 sakin layi na 8-9)
Idan muka saurari Yesu, za mu amfana daga hikimarsa (K. Ma 8:32, 35; w09 4/15 31 sakin layi na 14)
2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
(minti 10)
K. Ma 8:1-3—Ta yaya hikima take kira da “babbar murya”? (w22.10 18-19 sakin layi na 1-2)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?
3. Karatun Littafi Mai Tsarki
(minti 4) K. Ma 8:22-36 (th darasi na 10)
4. Komawa Ziyara
(minti 4) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Wani da yake so ya halarci taron Tunawa da Mutuwar Yesu ya yi maka wata tambaya game da taron. (lmd darasi na 9 batu na 3)
5. Fara Magana da Mutane
(minti 3) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ku marabci mutumin da ya zo taron don ya ga takardar gayyata a bakin ƙofarsa. Kuma ka shirya yadda za ka amsa tambayoyinsa. (lmd darasi na 3 batu na 5)
6. Ka Bayyana Imaninka
(minti 5) Jawabi. ijwbq talifi na 160—Jigo: Me Ya Sa Aka Kira Yesu Ɗan Allah? (th darasi na 1)
Waƙa ta 105
7. Bukatun Ikilisiya
(minti 15)
8. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya
(minti 30) w23.3 17-19 sakin layi na 9-16