RAYUWAR KIRISTA
Jehobah Zai Ba Ka Karfin Zuciya
Shin ka taɓa jin tsoron yin wa’azi ko ka gaya wa mutane cewa kai Mashaidin Jehobah ne a makarantarku? Idan haka ne, ta yaya za ka kasance da “ƙarfin hali” don ka yi wa’azi? (1Ta 2:2) Me ya sa kake bukatar ka kasance da ƙarfin hali? Bayan kun kalli bidiyon nan Jehobah Zai Ba Ka Ƙarfin Zuciya, ku amsa tambayoyin nan:
-
Labarin wace ce a Littafi Mai Tsarki ya taimaka wa Safiya ta yi ƙarfin hali?
-
Ta yaya kwaikwayon da Safiya ta yi da iyayenta ya taimaka mata?
-
Me ya sa yake da kyau ka yi wa ’yan makarantarku wa’azi?
-
Idan kuma ba ka makaranta, wane darasi ne ka koya daga wannan bidiyon?