Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ku Riƙa Nuna Ƙauna a Iyali

Ku Riƙa Nuna Ƙauna a Iyali

Ƙauna ce take ƙara danƙon zumunci a iyali. Idan babu ƙauna a iyali, ba za a kasance da zumunci da haɗin kai ba. Ta yaya maza da mata da kuma iyaye za su riƙa nuna ƙauna a iyali?

Maigidan da yake ƙaunar matarsa zai yi la’akari da bukatunta da ra’ayinta da kuma yadda take ji. (Afi 5:​28, 29) Zai kula da bukatun iyalinsa, kuma hakan ya ƙunshi taimaka musu su kusaci Jehobah. (1Ti 5:8) Matar da take ƙaunar mijinta za ta yi masa biyayya kuma ta “girmama” shi. (Afi 5:​22, 33; 1Bi 3:​1-6) Dole ne mata da miji su riƙa gafarta wa juna. (Afi 4:32) Iyayen da suke ƙaunar yaransu suna kula da kowanne cikin yaran kuma su koyar da su game da Jehobah. (M.Sh 6:​6, 7; Afi 6:4) Waɗanne matsaloli ne yaran suke fuskanta a makaranta? Yaya suke bi da matsi daga tsararsu? Idan akwai ƙauna a iyali, membobin iyalin za su sami kāriya da kwanciyar hankali.

KU KALLI BIDIYON NAN KU NUNA ƘAUNAR DA BA TA ƘAREWA A IYALINKU, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Ta yaya maigida yake kula da matarsa kuma ya nuna cewa tana da daraja a gare shi?

  • Ta yaya matar kirki take nuna cewa tana girmama mijinta?

  • Ta yaya iyaye suke koyar da yaransu Kalmar Allah?