Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ƙauna Ce Take Sa Jehobah Ya Yi Mana Horo

Ƙauna Ce Take Sa Jehobah Ya Yi Mana Horo

Horo ya ƙunshi ba wa mutum umurni da koyar da shi. Ƙari ga haka, ya ƙunshi yi wa mutumin gyara ko kuma tsauta masa. Jehobah yana mana horo don mu iya bauta masa yadda yake so. (Ro 12:1; Ibr 12:​10, 11) A wasu lokuta yana yi mana wuya mu amince da horo da aka yi mana, amma za mu sami albarka da amincewar Allah idan muka yi hakan. (K. Ma 10:7) Me ya kamata waɗanda suke yin horo da waɗanda ake musu horo su tuna?

Mai yin horo. Ya kamata dattawa da iyaye da ma wasu su yi koyi da ƙauna da kuma alherin Jehobah sa’ad da suke yin horo. (Irm 46:28) Ko da horon da za su bayar mai tsanani ne, su yi hakan da ƙauna kuma bisa yanayin mutumin.​—Tit 1:13.

Wanda ake wa horo. Ko ta yaya aka yi mana horo, bai kamata mu ƙi horon ba, amma mu yi amfani da shi nan da nan. (K. Ma 3:​11, 12) Da yake mu ajizai ne, muna bukatar horo kuma ana iya yi mana horo a hanyoyi dabam-dabam. Muna iya samun horo daga abin da muka karanta a Littafi Mai Tsarki ko kuma abin da muka ji a taro. A wasu lokuta kuma, wasu za su bukaci horo daga kwamitin shari’a. Idan mun amince da horo kuma muka aikata shi, za mu yi rayuwa mai kyau a yanzu kuma mu sami rai na har abada.​—K. Ma 10:17.

KU KALLI BIDIYON NAN JEHOBAH YANA YI WA “DUK WANDA YAKE ƘAUNA” HORO, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Wace tarbiyya ce aka ba wa Canon, kuma ta yaya rayuwarsa ta canja daga baya?

  • Ta yaya Jehobah ya yi masa horo da ƙauna?

  • Ka riƙa amincewa da horon Jehobah

    Waɗanne darussa ne muka koya daga labarinsa?