DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Ku Mai da Jehobah Mafakarku
An tanadar da biranen mafaka guda shida a Isra’ila don waɗanda suka yi kisa ba da gangan ba (L.Ƙi 35:15; w17.11 9 sakin layi na 4)
Dattawan Isra’ila ne suke yin shari’a (L.Ƙi 35:24; w17.11 9 sakin layi na 6)
Biranen mafakan suna kāre mutane da kuma tsare su (L.Ƙi 35:25; w17.11 11 sakin layi na 13)
Kamar yadda wanda ya yi kisa ba da gangan ba zai yi sadaukarwa sosai kafin ya sami kāriya a biranen mafaka, mu ma dole ne mu yi sadaukarwa kafin Jehobah ya yi mana jin kai kuma ya gafarta mana.