Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Kada Ka Bar Sha’awoyinka Su Zama Maka Jaraba

Kada Ka Bar Sha’awoyinka Su Zama Maka Jaraba

A matsayinmu na ’yan Adam ajizai, yana yi mana wuya mu kame kanmu. Kuma idan muna yin abin da muka ga dama, Jehobah ba zai amince da mu ba. Alal misali, wasu mutane sun fi son abinci ko kayan sakawa ko gida fiye da Allah. Wasu kuma suna gamsar da sha’awarsu ta jima’i ko da haka ta saɓa wa dokar Allah. (Ro 1:​26, 27) Ƙari ga haka, wasu suna barin mutane su rinjaye su domin suna so mutanen su so kuma su amince da su.​—Fit 23:2.

Ta yaya za mu iya kame kanmu? Wajibi ne mu riƙa yin abubuwan da za su faranta wa Jehobah rai. (Mt 4:4) Kuma mu roƙi shi ya taimaka mana. Me ya sa? Domin Jehobah ya san abin muke bukata kuma ya san yadda zai biya bukatunmu.​—Za 145:16.

KU KALLI BIDIYON NAN KADA KA KASHE KANKA DA HAYAƘI, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Me ya sa wasu mutane suke shan taba?

  • Mene ne illar shan taba?

  • Me ya sa shan taba ko na zamani irinsu shisha yake da haɗari?​—2Ko 7:1

  • Za ka iya gujewa sha’awar shan taba!

    Ta yaya za ka ƙi ko kuma ka daina shan taba?